ABNA24 : Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a cikin watan janairun shekarar 2019, jami’an tsaron kamaru suka tsare Kamto tsawon watanni 9, bayan da ya jagoranci zanga-zangar adawa da sakamakon zaben shugabancin kasar na shekarar 2018, wanda ya sha kaye a hannu shugaba Paul Biya.
Baya ga neman zaman lafiya a yankunan masu amfani da turancin Ingilishi, wata karin bukatar ‘yan adawar na Kamaru ita ce yi wa dokokin zaben kasar kwaskwarima.
Cikin sanarwar baya bayan nan, jagoran ‘yan adawar na Kamaru damagoya bayansa, sun sha alwashin jagorantar wata gagarumar zanga-zangar ta neman tilasta wa shugaba Biya yin murabus, muddin yaki amsa jerin bukatun da suka gabatar masa.
342/